Mai Biɗa Ya Bar Jin Gajiya: Tsokaci a Kan Bincike na Haƙiƙa a Fagen Ilimin Zamani
Wannan maƙala mai taken: “Fasahar Bincike na Haƙiƙa: Jagoran Ɗalibai Cikin Aikin Bincike.” Bincike na haƙiƙa shi ne irin nau’in binciken da ake yi na ilimi. Wannan bincike dai shi ne gano wani abu da ya faku ko ya ɓoyu a wani sashen na daban. Manufar wannan maƙala ita ce fito da aikin bincike na haƙiƙa da matakan da za a bi wajen yin sa. Haka kuma wannan maƙala jagora ce ga ɗalibai masu aikin bincike. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙalar ita ce, ta karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu na ilimi daga makarantu daban-daban. An kuma zaɓi a ɗora wannan binciken (Maƙala) a kan ra’in kwaɗaitarwa (Motivation Theory) wanda aka fi danganta samuwarsa daga MC Dougal, (1871). Sakamakon binciken da wannan maƙalar ta fitar shi ne, an gano cewa bincike na haƙiƙa yana buƙatar bin wasu matakai da suka danganci duban matsala, ziyarar muhallin da za a gudanar da wannan bincike wato inda matsalar take, tattaunawa da wasu masu ilimi kan abin da ake bincike a kai, samun kayan aiki, (data), yin amfani da fasahar zamani (SPSS) domin nazartar kayan aikin (analysis), fitar da sakamakon abin da aka bincika.
Authors
- Habibu Lawali Ƙaura
- Haruna Umar Maikwari
Publication Details
- Journal
- TASAMBO JOURNAL OF LANGUAGE LITERATURE AND CULTURE
- Published
- 2024-09-21
- DOI
- https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.025
- Primary Topic
- Hong Kong and Taiwan Politics
- Type
- article
- Field-Weighted Citation Impact
- 0.00