Tubalin Zambo Da Habaici a Zubin Ɗiyanwasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

Manufar wannan takarda ita ce, zaƙulo dubarun zambo da habaici kamar yadda suke ƙunshe a cikin wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru tare da nuna yawan aukuwarsu a cikin waƙoƙinsa. An yi amfani da dabarar bincike ta saurare aka saurari wasu waƙoƙi bakwai (7), aka kuma juyesu a takarda don tattara sakamakon bincike. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike bisa ga ra’i na tarken Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wato Gusau (2023) wanda Gusau ya fara ya samar 2003 ya jadadda a 2011, 2014 da 2015. Sai kuma ya sabunta shi a 2023. Haka kuma, Bahaushen Ra’i a wasu wurare dai-dai gwargwadon fahimta. Saboda masana kamar su Bunza, (2018:2), Tudun wada (2006), Malunfashi, (2014:50) da Koko (2011:3) a ruwaitar Ado, (2020) suna ganin cewa: “Hikimomi da Fasahar Hausawa tana nan a karin maganganunsu. Don haka, ana iya samar da ra’i a nazarin Hausa daga karin maganganun Hausawa idan har an yarda a yi hakan”. An kuma samar da sakamakon bincike ta hanyar yin amfani da ihsa’iyar bincike ta “Kashi cikin Ɗari”. Wannan takarda ta gano cewa makaɗa Sa’idu Faru ya kan yi amfani da hikimarsa ya yi zambo ko habaici ga Sarakuna, da ‘Ya’yansu, da masu riƙe da muƙaman sarauta, da fadawa, da kuma sauran jama’a, don ya isar da saƙo ga jama’a. Takardar kuma ta gano yawan aukuwar tubalin zambo da habaici a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa. Yayin da Tubalin zambo ya auku sau kashi 38% cikin ɗar,i shi kuwa, Tubalin habaici ya auku sau kashi 33% cikin ɗari, a cikin waƙoƙin da muka gudanar da nazari a kansu.

Authors

Publication Details

Journal
TASAMBO JOURNAL OF LANGUAGE LITERATURE AND CULTURE
Published
2024-08-31
DOI
https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.029
Primary Topic
African history and culture studies
Type
article
Field-Weighted Citation Impact
0.00
Controls
|||
ALL TIME
JAN
FEB
MAR
APR
MAY
JUN
JUL
AUG
SEP
OCT
article

Tubalin Zambo Da Habaici a Zubin Ɗiyanwasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

Hafizu Hadi, Ashahabu Ɗantanin
TASAMBO JOURNAL OF LANGUAGE LITERATURE AND CULTURE
African history and culture studies
article

Tubalin Zambo Da Habaici a Zubin Ɗiyanwasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

Hafizu Hadi, Ashahabu Ɗantanin
article en

Abstract

Manufar wannan takarda ita ce, zaƙulo dubarun zambo da habaici kamar yadda suke ƙunshe a cikin wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru tare da nuna yawan aukuwarsu a cikin waƙoƙinsa. An yi amfani da dabarar bincike ta saurare aka saurari wasu waƙoƙi bakwai (7), aka kuma juyesu a takarda don tattara sakamakon bincike. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike bisa ga ra’i na tarken Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wato Gusau (2023) wanda Gusau ya fara ya samar 2003 ya jadadda a 2011, 2014 da 2015. Sai kuma ya sabunta shi a 2023. Haka kuma, Bahaushen Ra’i a wasu wurare dai-dai gwargwadon fahimta. Saboda masana kamar su Bunza, (2018:2), Tudun wada (2006), Malunfashi, (2014:50) da Koko (2011:3) a ruwaitar Ado, (2020) suna ganin cewa: “Hikimomi da Fasahar Hausawa tana nan a karin maganganunsu. Don haka, ana iya samar da ra’i a nazarin Hausa daga karin maganganun Hausawa idan har an yarda a yi hakan”. An kuma samar da sakamakon bincike ta hanyar yin amfani da ihsa’iyar bincike ta “Kashi cikin Ɗari”. Wannan takarda ta gano cewa makaɗa Sa’idu Faru ya kan yi amfani da hikimarsa ya yi zambo ko habaici ga Sarakuna, da ‘Ya’yansu, da masu riƙe da muƙaman sarauta, da fadawa, da kuma sauran jama’a, don ya isar da saƙo ga jama’a. Takardar kuma ta gano yawan aukuwar tubalin zambo da habaici a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa. Yayin da Tubalin zambo ya auku sau kashi 38% cikin ɗar,i shi kuwa, Tubalin habaici ya auku sau kashi 33% cikin ɗari, a cikin waƙoƙin da muka gudanar da nazari a kansu.

TASAMBO JOURNAL OF LANGUAGE LITERATURE AND CULTUREVol. 3(03)
Openalex Percentile: Top 80%
African history and culture studies
AI Navigator

Ask Laika to Summarize, Analyze, and Connect papers live on the map.

Summarize Papers & Methodologies

Extract key findings, datasets, and comparative methods across publications.

Benchmark Rankings & Visual Analytics

Rank top research institutions, authors, funders, topics, and journals by Field-Weighted Citation Impact (FWCI) and paper volume with instant charts.

Connect Distant Disciplines

Bridge topological clusters on the map to find hidden collaborative intersections.